31 Maris 2015 - 11:46
Kai Tsaye:Sakamakon zaben shugaban Najeriya

sakamakon zaben shugaban kasa da aka fafata tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan na PDP da Janar Muhammadu Buhari na APC

 

 

12:24 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Gombe, Prof Ibrahim ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 11 inda aka tantance masu kada kuri'a 515,828. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 361,245 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 96,873.

Jega cikin tsakani ya ja kunen dan PDP Godsday Orubebe

12:18 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Bayelsa Prof. Joseph ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 8 inda aka tantance masu kada kuri'a 384,789. A cewarsa, Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 5,194 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 361,209.

12:10 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Lagos Prof. Adewoleya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 20 inda aka tantance masu kada kuri'a 1,678,754, inda jam'iyyar APC ta samu kuri'u 792,460 sai kuma jam'iyyarPDP wacce ta samu kuri'u 632,327.

11:58 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Niger Prof. Ambali ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 25 inda aka tattance masu kada kuri'a 933,607. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 657,678 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu 149,222.

11:52 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Ebonyi Prof. Ahaneku ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 13 inda aka tattance masu kada kuri'a 425,301. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 19,518 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu 323,653.

11:45: An ci gaba da karanto alkaluma, Prof Jega bai nuna wata damuwa ba kan wannan zargin da 'yan PDP suka yi masa.

Yadda Orubebe ya tayar da hatsaniya

11:31 Hatsaniya a cikin zauren tattara sakamakon, Mr Orubebe ya na cikin karensa babu babbaka, jami'an tsaro sun ki cewa komai a kai.

11:26 Wakilin jam'iyyar PDP a zauren tattara sakamakon zabe Elder Godsday Orubebe ya nemi ya ta da taron, inda ya ce jam'iyyar PDP ba ta gamsu da rawar da shugaban INEC, Attahiru Jega ke taka wa ba.

11:18 An bude zauren sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a cibiyar tattara sakamako a Abuja inda shugaban INEC Attahiru Jega ke kan babbar kujera.

Miliyoyin 'yan Najeriya na lissafa yawan kuri'u a wayarsu

11:10Alkaluma

A halin yanzu tsohon shugaban mulkin soji Muhammadu Buhari ya samu kuri'u fiye da shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

  • Janar Buhari na jam'iyyar APC ya lashe kuri'u : 8,520,436
  • Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP: 6,488,210

11:00 'Yan Najeriya sun kwana suna tunanin yadda za ta kaya game da sakamakon zaben shugaban kasar. Shugaban hukumar zaben Attahiru Jega ya ce za a ci gaba da sanar da sakamakon zaben a yau da karfe 10 na safe. A jiya dai an sanar da sakamakon zaba a jihohi 19 da kuma birnin tarayya Abuja. A yanzu ana jiran sakamakon zabe na jihohi 17.